ASHE KAINE MIJINA?
NA HAUWA M. JABO
By Alieyou_Abokie
Inna ta saka salati tana tafa hannu, dama nazia da nace kije ki musu sallama bakije kin musu sallama ba, yar duniyar ta qara kyalkyalewa da dariya, amma anyi shaqiyiyar yarinya inji inna, ta kawo min duka amma ina na kauce, na qara kyalkyalewa da dariya, mutuniya banza, sai ta ishimutane da dariya sai kace mai tabin jinnu, yaya ya gama qufula, baice komai ba.!!! Na zabga a guje ina ta dariya, ina shiga dayar kwanar na daure fuska, kamar banice mai kyalkyala dariyannan ba, na gyara hijabina nashiga gidansu hafizun birni mamanshi tana ganina ta hau washe baki,tana min kirarin da ta saba amma ko ajikana nasha magani abina tace auta matar auta, badai tafiyar ceta tashiba, kamar banason magana na kebe baki nace, E, tace yar nan Allah ya kaiku ya lafiya gashi sameer baya nan da sai in ce ya baki number yayan naki nura idan kunje sai ku nemishi ku riqa qaisawa, bance mata komai ba, ta qare surutanta, nace zamu wuce su yaya hafizu suna jirana, tace to yar nan Allah ya miki albarka, ta bani kudi wai insha ruwa a hanya amma naqi in karba, nace ina fati take? Allah sarki bata dawo makaranta ba idan ta dawo xan fada mata kun tafi, xatayi kewa Wallahi xan wuce yarnan baxaki karbi kudin ba nagode hajiya, dama itama ta sanni da taurin kai aranta take cewa tauri da tauri sai qaqa.. ......
Itama inna taga rashin dacewar hakan abu ya hade masa biyu ta miqe tsaye ke nazia tashi ki shiga mota kaima wuce mu tafi sumui sumui kamar munafuka na miqe zan dauki jakar kayana yaya ya karba inna tace sake mata kayanta ta dauka da kanta, Lallai ban kyautaba kuma duk ni na janyo amma......
Ki fito mun iso naji ya fada cikin sassanyar murya, tausayinsa ya qara kamani, ban san lokacin da na masa murmushiba, amma sam fuskar sa bata kaina, gidan da na gani ya tsoratani, wani fakacecen gidane, da gate yaya ya bude, muka shiga, naga ikon Allah araina nace a cikin wannan gidan zamu zauna, sabida ko a mafarki ban taba ganina a iran wannan gidan ba, gidane bangare biyu ban gare daya an kammala ginin dayan banqaren kuma ba'a kammalaba amma wanchan bangaren da ba'a kammalaba yafi banqaren mu girma, muka shiga, muna shiga na tabbatar da yaya yamin gatan da yake fadar zai mini, naga so da qaunar da yace zai nuna mini, tabbas nayi sa'ar dan uwa, wasu hawaye suka sake zubomin, yaya ya shigo da kayan mu, ya nuna min dakina komai a tsare hattana kayan make up an saka min toilet dina sai wanda ya gani dakin inna ma haka komai tsab an gyara, sai dayan dakin da ya nuna mana na baqi, ya nuna ma inna kitchen da kayan abinci da komai a ciki duk da tana daure masa fuska yana mata bayanin komai nima yamin bayanin komai amma yaqi bari mu hada ido yayi waya ya.........,
ga ciwon kai buguwar da nayi, nasan ba taxin da zata daukeni haka dame dame da kwata in bata mishi mota, nasan ko na sami mota banida ko kwandala, haka naja jiki na rabe jikin gate din wani gida, ina tsaye sai ga wata mota tazo music ne yake tashi sosai, saida suka iso kusa dani suka tsaya suka kwashe da dariya, nadago na kallesu, bance komai ba ba bakin musu tsiya, sukayi horn aka bude musu suka shiga gidan, araina nace dole in bar nan gurin
Dan yaran gidannan da alama basuda kirki dagani yan iskane, na duba gabas da yamma ba mafaka sai nan, sai kawai na haqura har a qare ruwan kunyar duniya ta isheni, jikina duk kwata, ga ciwon kai ya tsananta har na kasa tsayuwa na tsuguna, ruwa yaqi zaqaitawa sai......
ASHE KAINE MIJINA 20
Na HAUWA M. JABO
By Alieyou_Abokie
Gatachan dakina, mi takeyi a dakin ki kuma da gudu ta qarasa, tana ganina ta rungumeni, duk da warin kwatar bai saki gashinaba, amma haka ta rungumeni tana kuka,kin bani wahala naziah, ta janyo hannuna muka shiga daga cikin gidansu, dagyar nake tafiya, ga sanyin da nakeji, mun shiga gidan kenan, bamu kai parlour ba naji murya daga baya ke ina kika samo wannan almajirar??
Sista khade ta kalli nazia tace, ke dama yar akuyace??? Wacce batasan darajar na gaba da itaba?? Wallahi da nasan ke butuluce da bazan taba qawance da yar qauye irinkiba.!!
Mamakin duniya ya cika nazia dama haka sista khade take mara mutunci to ba gyaleta zanyiba, wata zuciyar tace ki gyaleta gidansu kikaxo, sista khadee sai masifa takeyi, inda take shiga ba nan take fitaba, zuciya ta rufe naziah uncle yayi Sokoko yana saqa Wulaqancin da xai mata, ni kuma ga mugun jirin da ya qara tasomin ga sanyi inaji ga yunwa, na dunqule hannu nakaiwa sista khadee wani wawan nushi, kuma na kamata da duka baki, sai jini, unle yana tsaye riqe da kumatu yana dada kallon wai almajirace zata mishi wannan wulaqanci yana chi gaba da saqa sharrin da zai mata kuma yasa a ma danginta wulaqanci, sai ganin yayi ana kokowa, tuni ya hanbare ni a wurgar dani gefe, ina miqewa na kama hanyar dana ga na biyo mun shogo na samu na fita gidan nakama hanyar titi kamar mahaukaciya, ga warin kwata gashi ina layi kamar yar maye, gashi banida ko kwandala na shiga taxi, ina tsaye idona sun fara rufewa naji qarar mota gabana, sai jin nayi yace ina zuwa na fada mishi unguwarmu tuni ya bude min nashiga........
ASHE KAINE MIJINA.23
Na HAUWA M. JABO.
By Alieyou_Abokie
Lallai khadija ba qawar kirki bace, wannan duk araina nakeyi, na dago na kalli mutumin nan,na rasa irin rashin kunyar da xan surfa mai, kawai, nace uncle to sista khadee ta gayawa inna da yaya ina gidansune??, sabida inna tace kada in kai maqreeb gashi har gari ya kusa wayewa?? Yayi kasake yana kallona, kayi magana mana uncle, yaji dadin sunan data kirashi dashi, har yana maimaitawa a fili uncle.!!! amma kuma shi wacce sista khadee ce take fada haka, Lallai idan yagaya mata baisan sista khadee ba wannan rudaddiyar zata daga mishi hankali fiye da na yanxu, amma zai lallabata har gari ya waye sai ya mata bayanin komai, da sanyin murya yace ki zauna in miki bayani, kinji sister na, da jajayen idona na dago na kalleshi jin ya fadi sunan da yaya yake kirana dashi, sai na sami kaina ina maibin umurninsa, na zauna girmn kai ba nawa bane na xauna.,........
Ya tsaya bakin qofa ya toge, ina tsoron in shigo ki mareni! Ko ki dakeni dan nakula bakida lafiya!! Naji xafin maganar amma na Shanye yaci gaba idan haukar taki baxata motsaba in shigo, kuuuuut dan na mareShi xaicemin mahau kaciya, na daqo na kalle shi namai kallon raini har na hada baqar maganar da xan yaba mai, kawai na sunkuyar dakai kayi haquri uncle.....
Yana xama ta fara jero mai tambaya...
Miyasa ka ijiye ni anan??
Mi kakeso in maka??
Baka tsoron Allah ne??
Ko kai ba musulmi bane??
Baka tunanin halinda iyayena zasu shiga??
Is ok.... ya katseta, da daga mata hannu kansa na kallon qefe, ta dago ta kalleshi, ki natsu kiji mi zan gayamiki!! Na farko Idan na fara magana kada kiyi magana sai na qare, kinajina? Eh naji!! Ya juyo ya kalleta tausayinta da yanda ta bashi amsa ya kamashi , lokaci daya sonta da sha'awar kusantarta ya kamashi, ya hade yawun dole, gashi ta wani mishikyau, tufafin sa ne a jikinta top da wando, yayi sauri ya kawar da kai, ya miqe tsaye idan har ya kuSan ceta bai mata adalciba, dan kuwa yayi niyar keta mata mutunci ladar mari da ta mishi amma kuma tausayinta ya rinjaye shi, ya miqe anjima zan miki bayani, zatayi magana, mi nace miki?? Ta tuna yace kada tayi magana, ta kalleshi taga idonsa taga ya kada yayi jaa, sai taji tsoro, ya fita, mamaki ya kamata yanda ya sauya lokaci daya, taci abincin tayi sallar tana nan zaune sai gashi ya shigo, abin mamaki bai kalli ko gefenta ya zaune ya juya mata baya.....
ASHE KAINE MIJINA?? 31
Na HAUWA M.JABO...
By @Alieyou_Abokie
Guys sun wuce sai inna ta musu hannu har sun wuce Sosai sai suka dawo, da yake ina cikin motar ne, ki fito ga wasu yan samari nan na tsayar kinsan ba jin maganata zasuyiba, nafito suna zuwa suka fito motar su, sai dayan guyx din yace kace kamar kasan matar kuma kace tsohuwace, eh Wallahi kafa San yau tin safe nakejin faduwar gaba, qirjina sai dukan 3..3 yakeyi i don't know y!!! Yanxu ma Sai naji ya qaru, ita tsohuwar fa?? Share Ashe ba tsohuwa bace manyan kayace, suka kwashe da dariya, suna qoqarin tsallakowa, amma fa daga farko tsaHowar dana gani kamar na santa amma na manta inda nasan ta, any how tunda munzo mutaimaka musu kawai, inna dama tana ganin sun dawo ta ta shige mota abinta, abokin deen ya shiga motar yayi danne danne sai kawai motar ta tashi, tunda suka xo naji jikina ya chanxa na Kasa dago kai in kalle gefen da nakejin ana kallona, muje ko deen dayan abokin ya fada amma ina deen yayi Nisa,Na dago da gyar na kalle mai maganar nayi godiya zan zaga yace idan ba damuwa ki bamu number ki, murna kamar ta kashe deen, Lallai yayi dacen aboki da yake gane duk wata matsala tashi, na bashi number bada son raina ba dan kawai mutunchin da suka mana ne.....
ASHE KAINE MIJINA?? 32
Na HAUWA M. JABO...
By Alieyou_Abokie
Na kalleshi a raina nace wannan kamar wani gaula daga kallon mutane kuma sai Kasa magana!!
Nace bari in fada mar Sunan da inna tace babana yana kirana dashi,
M hulwah, wawoo nice name, yamin wani murmushi bansan dalilin da yasa naji rass ba,nima na maida mai, owk hulwatiy sai kinjimu, yana murmushi yana sosa qeya kamar mara gaskiya, suka wuce nashiga mota inna tace da ace sun ganni ko taimakon ma bazasuyiba, na kyalkyale da daria wallahi inna akwi ki da zance akanme bazasu taimakamikiba,? To Sunga tsohuwa, Haka mukayi ta hira har muka isa gida, muna isa naji saqo a whtasapp, na duba naga sabuwar number kawai sai nayi blocking din number, dan Banason shirme, kuma nasan ban bama kowa number naba,
Na duba number sai naga d Same number da aka kirani da ita aka mun magana ta whatasapp akamin sms, na bude nace salam,
Kamar yana jira dama, ya fara surutuai...
Haba hulwaty, ya zan kiraki kiki dauka kinsan kuwa abinda nakeji araina......???
Let me call u,
No ka barshi let us chat,
Why my hulwah??
Coz dare yayi yanzu!
Owk hulwaty,
Hakadai yayi ta yimin kalaman soyayyah masu kashe jiki, duk abinda yaake fadar yana feeling nima ina feeling dinsa but ni na barwa chikinane dan banga amfanin yin haka ba tamkar na bada kainane ranar farko, sai hmmm, da owk da lol nake tura mishi, bai barni barni nayi bacci ba sai qarfe uku na dare ni kaina bansan lokacin yayiba, kuma banji bacciba, zan iya cewa nafada tarkon son deen, koda nasan cewa ni matar wani ce, abinda ya hanani kula samari kenan a rayuwata, amma wannan karon an sami akasi sabida dare daya deen ya sacemin zuciya, sonshi ya kamani,wanda nima jabo na hango hakan a fuskar naxoon inna....
Inna tayi dariya, ina fa ya rabaki dashi tunda idan kinyi aure dole ki tashi ki yiwa mijinki girki, kamin yaje aiki...
Ba'ayi kam, to kingani ai sai na sami miji sannan zanyi aureko inna??, inna tace nuran fa?? Haba inna nura sona yakeyi??, nura damuwa yayi dani?? Ki duba fa shekaranmu uku hudu a garinnan bai taba kiranaba kuma kin tanbbatar da yana garinnan,hatta qauye idan yaje baya zuwa guna, sai kace mara gata haka xa'bashi ni kamar abar sadaka , ki kalla fa hadda ko batan da nayi sau daya yayi miki jaje, shima bayan Sati uku sannan ya kira, da ya damu dani da yazo ya dubani amma shiru ni gaskiya inna yanzu an daina wannan qauyanci auren hadi, auren qauye, nasan da ace baba yananan koshi bazai bari in aureshiba wallahi, yanzu fa ki duba inna ace t........ ke rufemin baki da shegen iyayin tsiyaa, ni zaki nunawa boko, wayewa taci ubanta! Wallahi ko kinqi ko kinso, sai kin auri nura, sabida marigayi yana cikin halin mutuwa saida ya jaddadamin kada in kuskura in raba aurennan matuqar ba shi nuran yace ya janyeba, to wallahi in gaya miki kinyi kadan kisa akalleni mutuniyar banzabaaa........!!!
ASHE KAINE MIJINA??3⃣5⃣
Na HAUWA M.JABO...
By Alieyou_Abokie
Ba abinda nake tunani illah ranarda za'a daura min auri da wani ba deen dina ba!
Haka na juyo jiki ba qwari na dawo daki naci gaba da kuka, gashi kiran duniya nayiwa wayar deen dina amma a kashe,!
Da wanne yakeson inji? Da baqin cikin auren wanda baya sona koda baqin cikin rabuwa dashi??
Yakenan???
Gidan su sister khadee ne tsohuwar qawarta da taso ta salwantar da rayuwarta ita da mugun uncle dinta amma ta ijiye akan cewa my be sun saida gidanne yayan nura ya siya, da yake bata shiga gidan ba, so bata san yanda gidan yake ba bare ta gane, kawai dai an yiwa gidan sabon fentine, sun shiga an mata nasiha maman nura da babasu da yayyenshi da matar yayanshi da duk danginsu suntofa albarkacin bakinsu, ana ta sakamini albaka ana dada cewa inyi haquri, aka kwasheni sai gidan mijina
Gashi duk wani salon sarrafa namiji ta koyo shi sai dai ba mijin kuma bata buqatar sa a tunanin ta anyitane dan deen dinta....
Bazan sami damar zuwa yauba, idan kin isa let me know..!! haushi ya kamani, ya zai turani wata qasa ni kadai, amma van damuba sabida nafi buqatar haka...
ASHE KAINE MIJINA 45
NA HAUWA M.JABO
By Alieyou_Abokie
ban farkaba sai guraren 11 na tashi na kimtsa mukayi break fast,
deen ya siyo min ticket daga abuja zuwa sokoto, shi kuma yace sai gobe zai dawo, bada son raina na rabu da deen dinaba amma ya xanyi dole in haqura,
sai guraren maqreeb yaya ya dawo muka gaisa dashi yaji dadin ganin yanda nayi kyau, autan inna waje ta karbeki, na kyalkyale da dariya, ai yaya waje ta hadune naijarmu ce sai a hankali..!! munyi hira sosai dasu, anan nakejin yaya wai zai auri Zainab khalifa, abin mamaki yarinyar da ya tsana kuma ya raina wai itace har yake ce mata honey a waya,Lallai soyayyah soyayyah ce,
ina zuwa sai bacci ya kwasheni, ban farkaba sai kusan asuba, nayi sallah nashiga aikin gida ko ina na gyara duk yayi qura na aikatu amma kuma gidan sosai yayi kyau gidan na chanxa mai fasali..
Na Shirya musu girki kala kala,
Cikin kayan da deen dina ya siyo min na fitar musu da tsaraba, sunxo sunji dadin ganina da sukayi na kula da matar yayan nura sai kallona take tana murmushi motsi kadan tace mini sannu, araina nace matar nan tana sona, naji dadin zuwan su, sun tafi sun barni da Kewa.....
Ai nasan kin isa Turkey Ya karanta sms din yayi dariyar mugunta nura kenan...
A Turkish naji dadin qasar duk da cewa ita ma akwai tsadar rayuwa amma tafi Cyprus arha..
sai da na shalle sati biyu anan, nayi kewar deen fiye da ko wane lokaci,kullum muna waya muna faranta ran juna, danma kar ya ga jarabata tayi yawa ya rainani da tuni nace ya biyoni Turkey,
amma dole in kama kai, ko yanzu dai na more, "wawiya"
Haka na qare zama Turkey na wuce India ba nura ba labarin sa nayi xaton xamu hadu koda sau daya ne amma ina...
a indiya nayi wata daya cur dan qasar tafi su dadi da kuma sauqin rayuwa, duk kudina da suka rage a India na qarar dasu...
, sukace to Allah ya dawo dashi lafiya, nayi waya da deen dina na gaya mishi ina abuja yace in kama hotel in jirashi yazo, haka kuwa akayi na kama hotel, shima gobe ya iso, aranar kwana mukayi muna abu daya, deen ya nuna min yanda yayi missing dina nima na nuna mar munji dadin juna.....Tir daku.😖
ASHE KAINE MIJINA ???4⃣8⃣
Na HAUWA M. JABO,
By Alieyou_Abokie
A mota matar yayan nuru take ma yayan nuru gulma wai inada ciki,
Kaga yaronnan mutumin banxa yana nuna ma mutane bai damu da naziah ba Ashe munafukin yana xagawa kaganta har da ciki, murna a gurin abban Fatima kamar me, kamar ma ba'ataba musu haihuwa ba, a hirar har an saka suna yaran da naziah xata haifa,
idan macene sunan mamar nura idan kuma namijine sunan marigayi baban naziah, kunji mutane da iyayi.....
Duk abinda deen dinta ya fada taga idan ta fadamai xai rainata my be ma yaqi sakinta sai kawai ta chanxa shawara ta tsara yanda xata mai haka kuwa akayi ta aika SMS tana jiran reply....
ASHE KAINE MIJINA ?? 49⃣
Na HAUWA m. JABO...
By Alieyou_Abokie
Nan take nura ya rubuta takardar saki ya ijiye ma naziah a hanyar dakinta,
murna kamar ta kasheta yau xata kai ga burinta,ya deen dinta xaiji idan yaji ta karbo takardar saki,murna ba'a magana,
kamar ta wuce gida amma sai tace bari dai ta cika alqawari kuma taga wannan nihal da akeji da ita,kowa xancenta yakeyi xata dawo karatu canada, kuma tace gidansu xata sauka...
Sai yau nake tuna cewa fa...
tunda nayi aure banyi al'adaba ko sau dayaba..
Sai yau nake tuna dan ciwon dane da yawan xaxxabin da nakeyi..
Yanxu nake fahimtar inajin cikin cikina kamar ana min motsi..
Sai yau na tuna duk kwanciyar da nake da deen dina a jikina yake xube min.....din bai taba amfani da condom ba!!!
Lokaci daya hankalina ya tashi lallai ni lafiyayyace kuma komai xai iya faruwa dani,
Kardai ciki nake dashi???
Bayan bincike bincike Dr ya gane cikine da ita Dr yaxo yana fada, ke kinsan kinada ciki amma bakixo aka dubaki ba sai yau, to lallai jaririnki yan......
ASHE KAINE MIJINA ??50
NA HAUWA M. JABO..
By Alieyou_Abokie
Dr dan Allah kataimakeni Dr ka rufamin asiri ya xanyi da rayuwata...!! shi Dr yadauka taji abinda ya fada ne na cewa yaron cikinta na cikin matsala kuma cikin xai iya xubewa ko wane lokaci.. hakan yasa yake bata haquri da magana tare da alqawarin kasan cewa Dr ta har ta Sami sauqi, ya rubuta maganguna da allurai da kuma abincin da xata riqaci...
dama bata tafi phone dinta ba,
Ta kira deen dinta, koda taxo ya kira har 8,ta kira
He'll hulwatiy ya kike ina kika shiga inata kira baki dauka ba.??
Hello ko baki jinane?? har xai kashe sai yaji maganarta a hankali,
Inajinka deen!!!
Lafiyan ki kuwa??
Naje hospital ne...!!
Subhanallahi hulwatiy mi yake damunki??
Waye bashi da lafiya??
Kimin bayani mana kinyi shiru...
Na fara magaba ka katseni shi yasa nayi shiru..!!
Sorry hulwatiy kinsan Banason abinda xai taba min lafiyar kine ko kadan, kece jina kece ganina.. kece duk wani buri na rayuwata...!!!
Talk to me please m hulwatiy.!!
Tayi ajiyar numfashi,
Daxu Dr y dubani...
Eh inajinki ci gaba, miyake damunki mi Dr yace??
Yace wai inada juna biyu...
What..!!????
Eh yace ciki nake dashi, haba hulwatiy,
Kidaina min irin wannan wasan mana!!
Kamar ya Wasa
Wallahi deen da gaske nakeyi.
Hankalin deen ya tashi matuqa, ya Rasa abin cewa,
Ok ki bari anjima xan kiraki yanxu inajin maganar wannan shasha shar tana zuwa kada taji mi muke fada!!
Amma ai yau Monday deen daxu kace min kana office ne!!!
Eh ina office inaga tanada buqatar kudine taxo gurina!!
Amma kace min baka taba ganinta ba ya akayi har kake gane muryarta.??
Anya deen!!!!
No kingane ai......
Sai taji sallamar mace a wayar kuma taji an kashe aranta tace ee naji muryar mace inaga ta biyo shine, sai bata gane komai, kuma bata taba tunanin yaudara a gurin deen ba.
Da farko kuma har taji tsoro,
Amma fa ita dole deen yaxo a xubar da cikin nan kamin tayi yun qurin barin gidan aurenta, aranta ta riqa saqe saqe har bacci ya dauketa
Miye mafita??
Mafita dayace kawai ka rabu da matar mutane kaje ka rungumi matarka!!!
Idan nayi haka anya na mata adalci???
Lallai nayi kuskure nayi jahilci tarayya da matar aure,
Haka ya qare tunanensa qarke ya yanke cewa xai rabu da ita kawai taSan yanda xatayi da cikin......
Ta duba wayam ba miss call ko daya abin ya bata mamaki matuqa. Ta daure ta kira shi sai na uku ya dauka,
Hello deen....
ASHE KAINE MIJINA ?? 52.
Na HAUWA M.JABO..
By Alieyou_Abokie
Hello...Kanajina kuwa?
Eh inajinki.!!
Ya naji kana magana fada fada.??
Waya tabamun kaine??
Kedai ki fadi abin da xaki fada kawai.!!
Tayi shock dajin wannan maganar a bakin deen, wanda daidai da rana daya bai taba mata koda gaddama ba bare ya mata baqar magana.!!
Tayi ajiyar xuciya,
Allah ya baka haquri, dama maganar cikinnan ne nace ya xa'ayi dashi.??
Kuma dama inason in gayamaka na karbi takarda sakina..!!
Deen yayi duuum jin wannan maganar ta hulwaty, Lallai maisha ta riqa tasha ba abinda yafi illa ya fatattaketa ta rabu dashi, amma ya mata adalci kuwa? Anya yiyiwa kanShi da son da yake mata adalci kuwa?
Anya xai ma iya rayuwa ba hulwar sa, xaka iya mana dayan xuciyar ta bashi amsa....
Takeshi daga dogon tunanin da ya tafi, deen kayi shiru deen!! ,
Yanda ta fadi maganar da murya mai Sanyi sai ta qara bashi tausayi.!!
No Inajinki ci gaba..
Ai na fadi duk abinda xan fada.! Kai nake jira...
Dama ke duk abinda mukeyi dake kinSan bakiyi planing ba??
Dan ki xubar min da mutunci yasa kikayi tarayya dani?
Akan me xaki bari ciki ya Shiga,??
Ta yaya xan aureki da ciki??
Sam bakiyi tunaniba kuma bakiyi naxariba, ni Muslimine baxan taba yin shirka gurin xubar da cikiba, Sabida haka kisan yanda xakiya da cikin ki, ki nemi mijinki kuyi Sulhu ya rufa miki asiri ba hannuna ac......
Deen kaine kuwa..!!? Ta Katse shi cike da mamakin abinda yake fitowa daga bakin deen mi yake Shirin faruwa da itane abin kamar a mafarki...
Ki saurareni ya fada yana mai daqa murya.!!
Daga yau Sai yau kada ki qara nemana..!! kadama ki qara nuna kinSanni.!! jahilar banxa wacce batada tunanin....
Bansan lokcin da wayar hannuna ta subucemin ba cikina ya fara juyawa na fadi qasa na fara rero kukan nadama...
Tabbas na jahilace tana kuka tana surtai,banida ilimi gaskiyan ka deen ni jahilace ina matar aure namaida wani namijin mijina ina xankai haqqin aurene??
Kadan daga axabar da Allah xaimin kenan kamin inje qiyama inchi ubana...
Chikinta yaci gaba da juyawa, sai ta fara xubar da jini,
Ta tabbatar da idan har ciwo yakamata anan sai dai ta mutu ba wanda xaikaita asibiti,
Ta rarrafa tun tana ganuwa taja mota sai hospital, kamin ta Isa ta jiqe sharkaf da jini, bayanta kamar ya bude..
Takasa qarasawa cikin sai kwasarta akayi akayi ciki da ita,
Likitoci sukayo kanta, aka mata allurai....
Lokacinda ta farka taji ana qara mata ruwa, Dr yaxo yana mata sannu,
Hajia naziah sai dai kiyi haquri munyi iya bakin qoqarinmu na ganin mun tsayar da xubar cikin amma abin yaci tura, qarke ma Sai mukaga idan mukayi wasa xaki iya rasa rayuwar ki, sai kawai muka miki allura cikin ya qarasa xubewa...
Wata hamdala tayi hadi da jin dadi, lallai Allah ya rufa mata asiri da ya xubar da cikinnan...,
Dr yace
Yanxu xamu baki allurai da yan magunna kuma yakamata ki sanar da mai gidanki halin da ake ciki, kamin mu sallameki,
No Dr maigidana baya gari kuma ni ba yar nan bace.! Tafada muryanta yana hadewa,
Dr ya kalleta yace to shikenan xaki xauna anan har zuwa gobe ko jibi idan kin qara Samun lafiya Sai mu sallameki...
Dr kayi haquri ka sallameni yanxu kaga banxo da phone dina ba kuma nasan mijina da iyayena xasuyi ta nemana hankakin Su xai tashi ataimaka min please Dr...!!
Hajiya baxai yiWu ba, duk da kinada cikakkaiyar lafiya amma ya dace kidan qara samun rest....
ASHE KAINE MIJINA?? 5⃣3⃣
Na HAUWA M.JABO...
By Alieyou_Abokie
Samu rest, duk yanda Dr yayi akan naziah ta bari har gobe idan taqara jin sauqu a sallameta ta tafi gida amma abin yaci tura, ta nace akan tunda tanada lafiyar ta gida xata tafi...
Dayan xuciyar ta ya bata Amsa Eh deen dinke malam naziah...
Any how mun tashi 1__0, tasha alwashin sai ta rama abinda ya mata...
"JIBI NIHAL XATAXO KI GYARA MATA DAKINDA XATA SAUKA" ....
Hakanan ta lallaba taje dayan banqaren ta dan gyara sama sama, ta koma dakinta, dama naziah akwai xama daki "kamar jabo"
Nura yasa an yo siyayyah abubuwa kala kala duk na tarbar nihal,
Naziah aranta taji tana son gani wannan yarinyar da ake axarbarbabin zuwanta...
kamin qarfe biyu ta kammala hada komai gida yayi fes dama fes yake girki kala kala ta hada duk na tarbon nihal, itama dai tadanyi wanka duk da yanayin yanda ta kode ta chanxa tayi wani iri da ita amma dai tayi kyau, abinka da kyakyawan mutum...
ASHE KAINE MIJINA.?? 54⃣
Na HAUWA M. JABO..
By Alieyou_Abokie
Aunty..!
Aunty..!!
Auntyyyyyyy..!!!
Ina kike gamu mun iso, muryar da taji kenan ana gwalla mata kira,
Shikam nura yana ijiye nihal ya fita dan kada naziah ta kwafsamai gaban m nihal....
Na'am ina zuwa... naziah ta bada amsa a taqaice..
Ta fito qamshin da taji Lallai tasan qamshin, amma tasan hancin tane yake yaudararta...
Tafito da Walwala abinda take gani gabanta yafi bata mamaki akan komai, ba kowa bace face tsahuwar qawarta da tafi tsana a rayuwar ta itada mugun uncle dinta wacce Sanadiyar su ta bata wato sista khadee, tuni ko wacce ta daure fuska naziah ta kalli s...khade a wula qance ina nihal take??
Nihal ta kalli naziah cike da mamaki da al'ajabi Lallai wannan naziah ce kuma itace matar uncle dina dama ance mata sunanta naziah...!!
Kuuut yau ake yinta..
Ko wacce na kallon yar uwar ta, nihal cike da mamaki tace nicefa nihal din,naziah tace miya kawoki nan gidan, suna cikin magana kawai sai ga nura ya shigo...
Nihal..!!
Nihal...!!
Ya Shigo da kaya niqi niqi a hannu yana kwalawa nihal kira..
Abinda ya gani shine ya bashi mamaki hade da daure kai, ledodin hannun sa duk suka xube,
Jikin Sa na rawa hadi da sarqe war murya ta tashin hankali hadi da tsori ya kalleta murya na dancing, ke miyaa miyaa kawoku gidanaaa.!!??
kinxo dan ki tarwa tsamin iyali na hadi da jin dadina ko??, waima uban wa ya baki address din gidana...!!! Naziah ta gama raxana jin yace miya kawota gidan sa, idan dai nan gidan sane to Lallai mijintane!!
Kuma shine uncle din sista khadee da yace mata almajira kuma ya mareta, shine mutun na farko data tsana a tarahin rayuwar ta.!!
Shine sanadiyar batanta.!!
Kuma shine mutumin da ta qara tsana second time a rayuwarta wanda yayi sanadin shiga tashin hankalinta..!!
Nura ya kalli nihal yace ke ina naziah ta shigane??
Nihal ta kallu uncle dinta cike da mamaki tace uncle wannan ma ai sunanta kenan fa naziah .. WHAT???
ASHE KAINE MIJINA.?5⃣5⃣
Na hauwa m. jabo...
By Alieyou_Abokie
Eh uncle itama sunanta nazia....
itace qawata da nake baka labari lokacin,
kuma itace wacce ta maka rashin kunya lokacin da taje gidan mu,
No bashi nake neman saniba nihal.! wai itace matar tawa???
nihal da mamaki ta kalli uncle dinta.! tace kaman ya uncle dama bakasan matar taka ba???
yayi shiru yarasa abinda xai fada...
ita nihal mamakinta shine wata hudu dayin auren baima tama sanin matar ba to ya akayi akace mata tayi ciki?? kuma uncle yace mata bai santaba baima taba ganintaba amma batayi tunanin abin yakai hakaba!!!
Dukansu sunyi churko churko kowa ya rasa abinda xai fada.!!
nazia taji tsoro matuqa tayi tunanin kada su mata wulaqancin dayafi wanda deen ya mata da wanda wannan tsohuwar qawar tata ta mata, tajuya xata koma dakinta ta tattaro kayanta ta wuce gida tunda dama ya saketa..
tayi taku biyu uku kikajita lauuuuu... ta fadi "nima jabo bansan miya sa ta fadiba" duk sukayo kanta nura jikinsa na rawa yake bubbugata amma ko motsi batayiba hankalinsa ya tashi matuqa suka yayyafa mata ruwa amma inaaa shiru da sukaga xasu bata lokaci sai suka dauket
sai asibiti....
a hanyar asibiti kamin a isa ta farfado taganta a mota tayi yunqurin miqewa xaune taji an dan daneta irin ta kwanta dinnan a jikin wani qamshin da takeji yana dukan hancintane ya tabbatar mata cewa tana tare da deen ne ta daqo dagyar tana dubawa taganta ashe jikin deenma take kwance...
Nace a saukeni anan!! Wannan karo da gadara hadi da isa ta fada tare da tsiwa irin tata,
komai ta fanjama fanjam...
deen ya tabbatar da xata aika yacema nihal ta tsaya tafita ta basu wuri...
nazia tamai kallon banxa. dawa xa'abarka???
ASHE KAINE MIJINA.?5⃣6⃣
Na hauwa m. jabo.
By Alieyou_Abokie
ta katseshi da sheeeeee....!!!
yimin shiru munafuki macucu mayaudari lokaci daya ta kirashi da sunayen ta bude marfin motar da qarfi ta fita abinta...
yafito yabita a baya har xata shiga taxi yaja ya tsaya yabita da kallo hadi da kallon cikinta lokaci daya Allah ya sakamar qaunar cikinta fiye da yanda yake tunani...
nihal nason tayi magana amma kuma yanda taga ya daure fuska ya wani chanxa sai tayi shiru...
chan kuma sun kama hanya tace uncle nifa bangane wannan abunba nakuba naga..
bakuma xaki ganeba...
ya bata amsa a taqaice, ta kalleshi ta gefe, har xata qara magana ya katseta..
kuma banason inji wannan abinda ya faru gurin kowa...!!
hmmmm..! nihal taci gaba da driving dinta,
uncle ina xamu tafi yanxu..
gidana!!
nanma amsar a taqaice ya bata..
To ai..
to ai me? look nihal kindameni da magana kibarni inji abinda nakeje pleaseeeeeeeee...! har suka isa bata qara mai maganaba...
inna tana tambayarta abinda ya faru dagyar ta iya bude baki tace nurane ya sakeni .!!!
Inna tasaka salati..! sakifa kikace!!! eh wallahi inna ya sakeni!!
inna tana ganin abin kamar bada gaskeba ko kuma mafarki,
to Ina takarda, nazia tadan taqaita kukan nata tace takarda tana gida namanta da ita, hankalin inna inyayi dubu ya tashi,
inna ta kalleta rai a bace kinga yanda kika dawo lokaci daya kamar mai jego!!?
qirjin nazia ya qara bugawa..
waima miya hadaku ne da har ya sakeki??
naci gaba da kukana ban bata amsaba inajinta tayi waya da yaya ta gaya mar abinda yake faruwa.
bansan abinda yace mataba kawai sai naji tace to sai ka iso ta kashe wayar...
taxo taxauna kusa dani, tayi tagumi chan kuma tace,
Allah dai ya saukeki lafiya amma wallahi yaronan baiyi halin iyayensaba, amma dai bari muji miya hadaku kamin ince wani abu. !!
Wani rasss naji dama inna tasan inada ciki kenan ?? to ya akayi suka gane inada ciki?
yanxu idan ma nace baitaba kusantanaba ba yarda xasuyiba lallai da sake....
ASHE KAINE MIJINA.?5⃣7⃣
na hauwa m. jabo.
By Alieyou_Abokie
na tashi xan shiga dakin inna kenan, sai sallamar yaya mukaji yashigi kamar an turo shi yayi jaaa kamar qauta😡 sai huci yake kamar wani kasa...
Ya mata adalci kenan??
yanxu ki.....
inna ta katseshi kai wai wane irin mutunne kai bakasan miye ya hadasuba kawai xakaxo kana ma mutane rigimar banxa, Ai ka bari ta mana bayanin miye ya hadasu har ya saketa sannan ka fara rigama rigimamme kawai.!
dan taxo tace yasaketa haka kawai ba fada ba komai xai saketa?? dukansu basason juna to katabbata akwai laifin kowanne su aciki kabari tayi bayani da bakinta, ta kuma nuna takardar sakin sai aji yanda xa'abullowa abin..
yaya yayi ajiyar xuciya ya nemi guri ya xauna, amma fuskar nan har yanxu a turnuqe,
ya kalleni cike da tausayi kiyi haquri nazia kidaina kuka Allah xai saka miki idan ya yaudareki ina takardar sakin naki,??
Nazia ta bude baki dagyar muryanta duk ya dushe..
yana gidan!
miyasa bakixo dashiba,
mantawa nayi dashi.
gobe xamuje ki dauko kayanki da kuma takardar Allah ya sakamiki!!, ana cewa ya natsu ashe da sauransa, ni da ganin idinsa nasan baida kirki mutum banxa ay dama nasan xaiyi fiye da haka....!!
Inna ta kalleshi rai a bace waikai lafiyanka?
waya gayamaka ana shiga tsakajin mata da miji.?? wallahi xasu baka kunya daga baya ana ma magana kamaida ni mutuniyar banxa...!
ai inna duk ke kika janyo tun farko ni banso auren nan ba amma kika nace sai anyi sannan yanxu ga wulaqncinda yaI mata kina cewa abari sai anga takarda, kawai inna kisa mana ido dan ba qara bari xamuyi mu maimaita kuskuren farkoba dole in nemawa qanwata yanci dan anga bamuda uba..!!
Karo na farko da yaya yaqi sauraren inna idan tana magana, haka idan tana magana ya maida mata amsa..
mamakin duniya yacika inna tasaki baki sululu tana kallonsa,
Lallai baitaba mata hakaba, kawai bari ta barshi har ya sauko sannan su fahimci juna....
ASHE KAINE MIJINA?5⃣8⃣
na hauwa m. jabo.
By Alieyou_Abokie
ya tashi fauuuu... har yakai qofar fita ya juyo ke nazia xo muje,
na kalli inna naga ta dauke mana kai na fuske abina nabi yaya ina dan dingishina.
part din yaya muka wuce da yake an gyarashi tunda yaya ya kusa aure da zainb khalifa.!
mukaje sashensa muka xauna a parlour yaya yaso yamin magana amma ganin fuskata yanda na harqitse yasa yaja bakinsa ya dinke, amma ransa a bace,
ki shiga dakina ki kwanta ni xan kwana anan kamin gobe muga yanda xa'ayi..
ba musu na amince dan bayana kamar ya bude dan xafi gashi na jiqe sharaf da jini, ina buqatar xagayawa in kimtsa jikina...
na tashi naje dakinsa..
direct bayi na wuce dan in gyara jikina saidai kuma ba pad sai da tissue nayi amfani na watsa ruwa na fito..
ina fitowa na nemi guri na baje.
abinka da mara lafiya ga gajiya nandanan bacci yayi awon gaba dani...
ya gama rudewa ya zare kamar wani dan gwaya..
dama hulwarsace matarsa??
dama itace a gidansa bai saniba??
yanxu tana dauke da cikinsa!
waima ya xaman cikin yake shege ko mai uba.!??
dana ba shege bane!
dana dan halal ne koda bada sanin junan mu muka sameshiba.! dayan bangaren xuciyarshi ya bashi amsa,
ina qaunar dana fiye da raina!
lokaci daya qirjinsa yayi wani mummunan bugawa daya tuna cewa ya saketa!!
ya tuna wulaqancin da yamata. anya xata yafemin kuwa??
bangaren xuciyarshi ya bashi amsa da xata yafe masa tunda tana sonsa!!
amma yana tunanin baxata taba yafe marba.....
yafi yarda da cewa baxata yafemar ba.
kuka ya saki kamar qaramin yaro ya durqushe qasa lallai na yaudari kaina na yaudari soyayyar da hulwaty ta nunamin...
ASHE KAINE MIJINA??5⃣9⃣
Na hauwa m. jabo..
By Alieyou_Abokie
waima da wane ido xai kalli iyayenta dama nashi iyaye iyayenta sun mai karamci tun tana jinjira ya nemi a bashi ita kuma aka bashi aka ijiyemasa ita tun lokacin har ta isa aure lallai ya xalunceta, koda baya sonta baidace ya mata abinda ya mataba, kodan karamcin da iyayen ta suka mai , mixaicewa iyayensa idan sukaji cewa ya saketa.!?
Lallai ya tsuke tunaninsa ya akayi bai ganetaba? ya akayi bai gane sunantaba..!? Ta taba gayamin sunanta nazia amma tace babanta yana kiranta da hulwa, so tafison sunan shi yasa bai gane sunanta na asali ba.
ya tuna lokacinda xai siyamata ticket daga abuja xuwa sokoto yaga sunanta Nazia muhammad amma baiganetaba.!
duk tunanin daya dauko baya kaiwa qarshensa, yaga ba yanda xa'ayi ya ganeta, amma hadda jahilci yayi mai yawa .
yanxu yatuna ya kirata hulwarsa da jahila ashe nine jahilin nine daqiqin nine axxalumin yaci gaba da kuka hadda gunji kamar qaramin yaro....
itakam ta rasa gane komai duk tunaninta bata samun amsa, lokacinda xata iso Mamanta tace kada ta riqa barin antin nata da aiki dan tanada juna biyi (ciki)
lokacin da taxo uncle da aunty nazia sun nuna basu ma san juna ba.!!
duk tunanin ta bata sami amsaba.
taja ta tsaya qofar dakinsa. tana tsoron ta shiga dakin ya balbaleta da masifa gashi ya gargadeta..
ganin kukan da yake ya tsananta da wani gunji da yake yasa bata tsaya wata wataba ta fada dakin taje gunsa cikin tsoro,
uncle miyake faruwa??
kamar baijitaba
ta qara maimaita tambayar har saida ta tabashi da qarfi sannan ya dago ya kalleta yanda taga ya chanxa ya hargitse lokaci daya abin ya bata mamaki da tsoro..
kodai yanada aljanune??
ta kalleshi uncle mi yake faruwa ??
ya kasa magana amma dai ya daina kukan da yakeyi,
ya dago ya kalleta abin tausayi dashi " koda ni jabo bancika jin tausayin maxaba dan basuda kirki amma yadan bani tausayi kadan😉" ya bude baki nihal xaki timakeni???.
Eh uncle xan taimakeka..!!
kinyi alqawari!??
Eh nayi..!
Duk wahala???
Eh.!!
nihal talk tome ina cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali kimin alqawari idan kowa ya gujeni ke xaki tsaya tare dani xaki rufamin asiri..!!?
Uncle na maka alqawari duk wuya duk wahala xan kasance tare dakai har qarshen rayuwata...!!!
idan na dawo xan kammala.
ASHE KAINE MIJINA 6⃣0⃣
Na hauwa m. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Yaji dadin alqawarin da nihal ta daukar masa yasan kuma akwai ta da jajircewa akan abinda takeso idan har ba wulaqanci a ciki. ta yarda dashi saidai tunaninsa daya ya xasu bullowa abin., ? Dolene ya gayawa nihal gaskiyar abinda ya faru anya zai iya kuwa? tabbas baxai iyaba zai tonawa kansu asirine kawai wannab sirrine tsakaninsu baidace kowa yajiba. zaidai san yanda zai bullowa abin. Nihal dai tana zaune tana kallon uncle dinta duk da ya daina kuka amma yana wani gunguni gunguni dukkan alamu dai ya zautu ta kira sunansa uncle ya dago ya kalleta, au kinanan? Ai
Kina iya tafiya, tace to, ta tashi ta tafi cike da saqe saqe a ranta haka yaci gaba da tunane tunanensa yana kuka har barci yayi awon gaba dashi..
Bai farka ba sai guraren asuba ya tashi idonsa sunyi hulu hulu ba kyan gani. Maimakon yayi sallah sai ya wuce dakin hulwarsa yana shiga ya dauki turarenta yana shinshinawa hadi da hugging din kwalbar turaren yana kwalla kamar wani xararre ya tashi yana yan tabe tabe tabensa har yakai gun wayarta battery low ta mutu ya jona chaji komi yake nema oho ya dauko hand bag tinda yana lakube anan yayi karo da takardar sakinta da magungunab.! vai duba maganin kona miye ba tunda yasan tanada ciki xai xama maganin masu cikine. Aranshi Wato bata tafi da takardar ba "yama manta da cewa suma tayi a hanyar hosptl ta farfado tace a kaita gida" lokaci daya baqin cikinsa ya dawo farin ciki yayi wani murmushi bada bata lokaciba ya shiga bayinta ya yayyaga takardar yayi xuba a bayi yayi bayan gida akai😀 ya kora rowa yayo alwula yaje yayi sallah... Allah kadai yasan abinda yake saqawa a ranshi har gari ya waye yana laximi akan Allah yasa ta yafe masa su dawo normal...
Yaxo ya sami nihal ta hada mai break fast bai iya ci sosai ba yadan taba dai kawai duk dahaka nihal tayi mamakin sakewar da yayi akan jiya. Nan xarginta ya qara tabbata akan uncle dinta yanada jinnu dan su suke haka one time kuma kamar ba'ayiba
Taso suyi magana sai kuma ta basar tunda jinnu ne baxai tuna komai ba....!!
Kije ki shirya muje gidan wancan yaro ki dauko takardar sakinki da kayan buqatarki.
No yaya muje a haka kayana duk suna chan gidan.
Kije ki duba wardrobe dina zaki ga kaya ki xabi daya ki saka
Naje dakin abin ya bani mamaki ganin kayan mata kamar wani qaramin store ta dauki wani dogon riga baqi ta saka duk da ta rame amma kayan su. Karbeta sosai.
Koda ta fito harya qare hada musu break fast ta xauna suka ci lallai taji yunwa rabonta da abinci tun jiya da safee.!!
Suka fito sukaje sashen inna suka gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa suka gaya mata zasuje gida nura in dauko takardar sakinna da kayana har sunkai bakin qofa inna tace ban yarda kuyi chin mutunci da kowaba yaya ya amsa da insha Allah..!
Suka isa unguwar tunda suka isa unguwar qirjinta yake dukan uku uku har suka isa gidan suka iske gidan a bude suka shiga nihal "sis khadee" sukayi karo da ita a palo tana chatting fuskarta cike da fara'a da gani ita da ammar suke soyewa koda bansan still suna tareba.
Tana ganin mu tayi shock xunbur ta miqe ta gaidamu cike da fargaba yaya ya amsa mata rai a sake direct dakina na wuce abu na farko danayi karo dashi yasa nasan an mini bincike dakin cike da qamshin turarena kamar anyi wanka dashi hand bag dina komai an juye a saman gado waya a chagi haka dai ta tattare kayanta na buqata amma ta nemi takardar sama da qasa bata ba labatinta.! wayarta ma dagyar ta ganta dan a chaji take ta fito a sanyaye tacewa yaya bataga letter dinba da kuma yanda ta sami dakin anan suka gane yayi bincike ne kuma shi yadauke takardar ran yaya ya baci matuqa ya kalli sista khadee ke ina nura?? Bakinta na rawa tace Yaje office ya dauko wasu takardu har suka gama xaman jira bai dawoba an kira wayar a kashe suka tafi gida sunje sun ma inna bayani tayi tagumi batace komai ba.
Anan aka xauna ake tambayata da wane dalili ya sakeni yaya yake cewa kodai da nihal kuka sami sabani nace aah na rasa abinda xan fada.......
ASHE KAINE MIJINA6⃣1⃣
Na Hauwa m. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Guraren maqreeb yaya ya dawo ya sameni nadan saki jikina baicemin komaiba har zai fita inna ta kirashi ta tashi ta shige daki ya bita baya bansan mi suka tattaunaba naga sun fito abinsu.
Ya qara wuta inna bata min magana nima bance musu komai ba har nayi Kwana biyu a gida. Ina duba wayata da yake na dan saki jikina kadan kuma na warware rashin lafiyarda nayi dan inashan magani akan kari. Ina karanta wani hausa novel a group din hauwa m jabo sai wata tace amata sending din wani pic ina dubawa kawai naci karo da hoton takardar sakina dana dauka zan nunawa deen lokacin dan inason inyi surprise dinsa.. sai yacimin mutunci yace bani bashi "dama na nuna mai tun lokacin zai gane tunda rubutunsane" sai naji maganar yaya da inna da guduna na fito na na nunawa yaya hoton takardar sakina yana dubawa baice komai ba ya ma inna bayanin takardar inna tace saina fadi dalilin sakina naga dai boye boye ba nawa bane sai kawai na bayyane musu komai na gaya musu bai taba kusanta naba yaya ya kalli inna inna ta kalli yaya cike da mamakin maganata sai inna tayi qarfin hali ke dan mijin ki ya sakeki kada ki maida mu mutanen banza, kinason kice cikin da kike dashi ina kika sameshi?? Ko kin dauka dan baki gaya mana kinada cikiba mu ba zamu ganeba ki chanza wata qaryar ba wannan ba.!!!! Inna ta karkade zaninta ta qara gaba ta barmu da yaya ya juyo ya kalleni yazo kusa dani ya zauna.
Ya dafa kafadata nazia kiyi magana ki fadi gaskiyar abinda ya hadaki da mijinki wani ki mai sharri ko qire ko qage duk bai taso ba ki fadamin gaskiya kinji autar inna! Na fara rantse rantse akan ba abinda ya taba shiga tsakanin mu dashi iya abinda na fada shikenan ba wani ciki da nake dashi kawai dai nayi jikine hatta honey moon da mukaje kowa da ban ya tafi abinsha haka dai nayita tona asirin zaman mu amma ban fadi yanda muke dashiba....
Yaya kam ya gamsu dan bai sanni da qarya ba dama shi baiga ciki ba inna ta bashi labarin cikin wacce akace tanada tace ba haka bane miye nasu na qarya tawa.
Ya shiga sukayi magana da inna ya fito ana maimaita maganar cike da jimami....
Zamu jirasu zuwa qarshen sati idan har danginsa basuce mana komai ba zamuje mu kwaso kayanki dan ba komawa zakiyi gidannan ba..
"kaji wauta irinta yara wai nihal zataje biko"
Nazia dai kam inna ta yarda ba tada ciki tunda bataga cikin ba yanxu kuma alamomi sun nuna haka tunda lokacin kullum idan sunyi waya da nura daga yace baya gida sai yace yana kan hanya sai yace tana bacci ko tana sallah hakadai bai taba baiwa nazia sun gaisaba kullum kwana kwana yake mata shima yaya ya yarda dan shima kusan haka ta faru ya kira nazia ina nura tace baya gida ya kira nura ya nazia yace tayi bacci bayan daidai likacin suka qare waya yayi tunanin wani abu saidai bainkawo komai a ransa ba haka dai kowa ya riqa fadin albarkacin bakinsa..
Nazia baqin cikin wulaqancin da deen ya mata yana damunta amma ba halin fada dan ita ta janyowa kanta sonsa ya rufe mata ido yanxu ga abinda ya mata tasha alwashin duk ya kuskura yazo gidansu sai tamai kaca kaca.
Yau suka shirya kwaso kayanta da la'asar guraren biyu saI ga nihal a gidan inna dai kam bata ganeta ba tace gun nazia tazo.
Inna ta kira mata nazia ta shige dakinta.
Nazia ta fito da fara'a wa zata gani maqiyarta sista khadee. Nazia Ta wani daure fuska tasha magani ta zauna akan hannun kujera ta dora qafa daya akan daya tana girgizawa tana shan sweet..... sis khade ta gaisheta ta amsa da lfy a taqaice.
Gunki nazo, aunty nazia idan zaiyiwu mu shiga daga ciki..
No.. Nan ma is ok nazia ta bata amsa ba tareda ta kalleta ba.
Ta hadiye yawu tayi qasa qasa da murya. Dama aunty akan maganar.......
Ta dakatar da ita da hannu...
Don't ever called me your aunty, am not & i will never be the one. I can hear you go ahead.! Ta qara kawar da kanta gefe..
Nihal Tayi ajiyar zuciya dama akan maganar uncle ne naxo dan Allah...... nanma ta qara katseta..
Shot your mouth up! you thinkless, do to most disgraced embrassemented matter you already done to me & your inrespective your mannerless, uncle do! But your came with another ovios alonatic thinking?.
to let me tell you, kije ki fada ashawon uncle dinki idan ya isa yazo da kanshi ke banida lokacinki wawaye kawai, ran sis khade ya bala'en baci taji maganar har cikin ranta tasosu kuma taji haushin maganganun nazia amma ba yanda ta iya tazo gyara tayi barna.??
Ta dago ta kalli nazia taga yanda ta daure fuska tasha jinin jikinta ta rasa abin fada chan nazia ta juyo.
Get out of this abode.! before I disgraced your personality now! Think less, stupid people haved to go and find an approach of manners & valuable of any mankind has wasing to you.
Oya ga hanya ta nuna qofa get out.!! Ta fada da tsawa.!
Sis khade ta gama qulewa tasan idan har taci gaba da zama faruwa naci ba nata bane mutuncinta yafi mata komai ta dauki jakarta ta fita kamin ta fita ta jiyo tsakin nazia think less kawai..!
Nazia tasani sarai sis khade batason tsaki tasha fada da mutane a secondary skull akan tsaki dan kuwa da kamata tsaki gara ka waska mata mari... har ta tsaya sai kawai ta wuce rai a bace...
Ta fada mota taja daqarfi tana fotowa gidan taja ta tsaya tana kwalla, lallai nazia taci mata mutunci da yake tasan weak point dinta shi yasa ta mata haka anya zata iya cika alqawarin da tayiwa uncle dinta kuwa da wuya dan bata daukar raini gun kowa wallahi. ta share kwallarta taci gaba da driving kamar zuciyarta ta fito dan baqin ciki ita zata cire hannunta dan tasan nazia da bala'en tsiwa komai zata iyayi..
Idan kuma ta juyawa uncle dinta baya wazai taimakeshi.?? Dayan xuciyarta tace wanda yasa ya saketa ya taimaketa..
ASHE KAINE MIJINA 6⃣3⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Da wannan tunanin ya isa gidansa koda taje ta tarar baya gidan ta tattara kayanta tayi gidan su, mamanta na ganinta taji tsoro kardai kun saida hali da matar uncle din naki?? Da yake ke nihal bakida hali ga zuciya kamar ta kasheki naga fuska duk a turbune...
Sis khade tayi murmushi ta nemi guri ta zauna to umma yau baki chankaba, ta kwashe duk abinda idonta ya gano mata ta fada musu kuma lallai alamu sun nuna baima taba ganinta ba itama haka.
Maman nihal tayi dariya.! kefa har yanxu yarinyace wata qila sabani ya hadasu amma mace hadda ciki kice basu taba ganin junaba. Nihal dai tayi qoqarin yiwa umna bayani har saida umma ta gamsu da dalilan da ta kawo mata dan kuwa taji har ya saketa da kuma ta fada mata da bakinsa ya fadi ya saketa din. amma kuma nihal din tace abinsa harda aljanu kam. Amma bari baban fati "abbansu nihal kenan" ya dawo muji yanda abin yake.
Bayan isha saiga nura yazo gidan yana neman nihal yaga gida wayam!! Ba nihal ba kayan naxia abin ya bashi mamaki wato ya tura nihal gyara ta maibarna ko?? Zai kuwa chi ubanta.!! ( kaji wawa) yaje gun maigadi a firgice yana tambayarshi ya haka maigadi yamai bayani daga zuwan nihal har zuwan su nazia yana qarewa nura ya wankeshi da mari kaji taaasssssss!!! kuma yace sai ya dawo da kayan da suka diba dan bai bashi umurnin barin kowa ya dauki komai a gidan ba! ((kaji hauka ina ruwan maigadi ai sai yace sai ya dawo mai da matarsa bawai kayan matarsaba😅))
Magadi yayi tsuru tsuru ya riqe kumce yana bada haquri nura ko saurarensa baiyiba yace yabar mai gidansa ya sallameshi ya wuce cikin gida a fusace. Dama su nura an iya kuka ya zauna tsakiyar palo ya fara kuka ba mai rarrashinsa cikin kuka ya jiyo magana sama sama koda ya duba sai yaga abban nihal tsaye yaxo gabansa yaja ya tsaya yamai kallon banxa ganin gidan ba kayan nazia ya qara tabbatar mai da cewa lallai ya saketa. Bai tausayawa halinda yaje cikiba ya haushi da masifa. Qarshe yace yadauka yazama mutum ashe har yanxu da sauransa! Sabida haka ya tattara kayansa ya bar wannan gidan dama albarkar nazia aka bashi wannan gidan nura ya tsananta kukansa basu barshi da baqin ciki rabuwa da mataraaba suna qara mai wani baqin ciki.
Yayan nura yayi waya gida ya fadawa mamansu da babansu abinda yaronsu yayi itadai kam maman nura da taji abin kasa magana tayi dan tsananin bacin rai... nura baiyi halacciba sai kallo kallon suke itada mai gari "baban nura" maman nura tace a kira inna amma mai gari yace wannan mugun abin ya wuce waya saidai su tafi. da kanmu har gidan. tun da asuba iyayen nura suka baro qauye sukaxo birnin sokoto. Bayan sun dan huta suka kwashi jiki sukaje gidansu nazia bawai biko sukaje sunje bada haqurine.
Koda Inna batasan zuwansuba ta musu tarba cikin mutunci da sakin fuska kamar ma ba abinda ya faru amma maman nura ta kasa koda hada ido da ita. Inna kam Sai neman ayi hirar bayan rabo takeyi amma duk sun kasa kunyar abinda dansu yayi ya ishesu. Chan dai maman nura ta fashe da kuka ta rungume inna tana bata haquri. Nura vai kyautaba! Baiyi halacciba.! Yaci amanar nazia.hakadai tayi ta sunbatu. inna nafadin babu komai har dai itama ta fashe..!! dan abin ya dade yana cinta inna kuka maman nura kuka dagyar dai mai gari ya samu ya rarrashesu sukayi shiru cike da kunya shima.....!!
ASHE KAINE MIJINA 6⃣3⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Suka kwashi jiki sai gidan su sister khadee mai gari yasa aka kirawo masa nura bai bata lakociba yaxo ganin yanda ya zama lokaci daya abin ya basu mamaki da tausayi.!!
Jikinsu yayi la'asar maman nura ta kalli autanta tama manta da aika aikar da yayi ta taso ta riqeshi tana tambayar lafitar shi. Ran yayan nura ya baci ganin yanda mamansu ta rude ganin halinda danta yake ciki ya daka mai tsawa hadi da cemai munafuki wallahi mama kuk kuke kulashi iskancine kawai.!! mama ta dalla ma abban nihal harara ta zaunar da shi. Palon yadau shiru chan mai gari ya fara yiwa nura bayanin abinda suka sani hankalin nura yayi mugun tashin dajin cewa tace basu taba hada shinfidaba, kuma batada ciki kenan ta zubar mai da ciki?? Cikin da ya daura ma son duniya.! Cikin da yake tunanin shine zai taimaka masa su gyara auren su. Ya saki wata irin qara saida kowa ya firgita a gurin yace.........
ASHE KAINE MIJINA 6⃣4⃣
Na Hauwa M Jabo.
By Alieyou_Abokie
sai kukan nura ke tashi a palon jikinsu yayi sanyi yayan nura yace dama nihal tace aljannu ne suka shafeka, inaga yafi kyau a bari sai yaji sauqi sannan ayi maganar. nura ya dallama yayan sa wata muguwar harara idonsa cike da hawaye sunyi jaa cike da fushi yace kaine mai aljannu baniba dama ka tsaneni baka sona daaga yau kai ba yayana bane..!! Duk palon saida kowa ya yayi dariya da maganar malam nura autan mamanshi... suka qara tabbatar da cewa yanada rashin lafiyar jinnu. dan kuwa ko musu bai taba hadasu da yayan saba kuma yana tsoronsa fiye da yanda yake tsoron iyayensa. Amma yana mai irin wayannan maganganu. kowa sai ya gasganta maganar abban nihal. Ya taso yaxo ya rungume qaninsa yana rarrashi cike da tausayi shi kuwa sai wani qace jikinsa yakeyi.!! Haka dai zaman ya qare ba wata natija.
Da dare maman nura ta bi nura dakinsa suna magana ya qara jadda dama abinda ya fada farko cewa bai saki nazia ba idan ya saketa kuma ina takardar saki?? Nan fa duk da cewa tana mai kallon mara lafiya ta gasganta maganar sa. Bayan ta fito ta samesu a palo suna tattauna maganar akan a nemowa nura magani anan maman nura tace idan har da gaske ya saki nazia ina takardar sakin take?? yaka mata fa idan za'ayi abinnan ayi adalci bai yuwa ace autana ne kawai bashida gaskiya
itama da laifinta. Sukayi shiru lallau yakamata ace ga takardar saki bawai kamar yan da inna ta musu bayaniba wai sakin a waya ne. Haka dai aka qare akan za'a nema mishi magani idan yaji sauqi sai a hadasu su biyu a aji gaskiyar maganar.!
ASHE KAINE MIJINA 6⃣5⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
An shirya zama kowa yazo hadda su nihal an hallara.
Aka fara maganar kowa ya fadi albarkacin bakinsa amma nura yaqi saukowa akan cewa ya saketa. Akayi sama akayi qasa amma yaqi yarda yace idan har da gaskene to ta kawo shaida a rubuce dan ba zasu yarda da waya ba, wannan zamanin komai ana iyayi. qarshe nazia taga ba nasara a gunta ta miqe taje daki ta dauko qur'ani tazo gabansa ta tsuguna ta miqa mai qur'anin tace idan har yayi rantsuwa da wannan qur'anin akan cewa bai saketa ba, zata koma gidansa yau dinnan.!!
Nura ya rasa yanda zaiyi sai zufa ke keto masa.!! Chan dabara ta fado masa ya karbi qur'ani yace zaiyi rantsuwa amma itama tayi alqawarin cewa zatayi rantsuwa akan cewa basu taba hada shinfidaba kuma bata dauki cikinsa wata huduba.
Qaqaqara qaqa....
Suka fara kallon kallo tsakaninsu palon yayi tsit ana sauraren wannan lamari nasu.! Nazia ta karbi qur'ani jiki a sanyaye tace kamin ka rantse ni zan rantse. ta riqe qur'ani hannu bibbiyu ta rufe ido tana hawaye...
Tace Ni nazia muhammad na rantse da darajar wannan qur'anin!! A matsayina na matar nura ta sunna bai taba kusantana da sunan raya wannan sunnar aure ba daidai da second daya saidai ya......... tuni nura ya taso yarufe mata baki ganin zata fallasa sa dayan mugun aikin da suka aikata.! wanda baya fatar hakan ta kasance har qarshen rayuwarsa.!! Bayason Iyayensa susan halinda ake ciki. Tausayin nazia ya kama kowa yayan nura ya haushi da fada akan me xaka hanata fadar gaskiya? ? Ta tabbata kenan bakada gaskiya.!! kamaida mutane sha sha shai. Yayan nura yazo gaban nazia yace mata nazia ci gaba saidaime??? Nura baisan lokacinda ya juye bakiba da harshen farisanci da suka koya tare da nazia tun kamin suyi aureba yace mata (( nazia turo khuda asrari moro pakhsh nakun na bi khatiri man bi khatiri khuda.....)) ta dago ta kalleshi harga Allah ya bata tausayib yanda ya hargitse da kuma yanayjn sautinsa ko banza tana sonsa ta kalli yayan nura tace mai ba komai. Nura yayi ajiyan zuciya yayansa ya kalleshi ya rasa bakin magana tunda baisan mi yace mataba.!! (( nima hauwa jabo saida na tambaya aka fassaramin abinda yace kuma bazan fassara mukuba 😁)) nihal ta taso taxo ta qarbi qur'ani itama tayi rantsuwa akan cewa lokacinda tana gidan uncle ya fada mata da bakinsa ya saki nazia yakai sau 50. Ta fadi yana yawan maimaita cewa ya yaudari nazia ta taimaka masa..... Mai gari yace kada ku maida qur'ani abin wasanku mana. Ya karbi qur'ani hannunun nihal ya koma ya zauna kowa yayi shiru ana jiran gogan naku nura mayaudari yayi magana amma kamar ruwa yacishi yayi tseeeeet....
ASHE KAINE MIJINA?? 6⃣6⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Baba lallai na saki nazia saki daya!! Lokacinda na saketa bansan cewa itace matar tawaba! Kuma ni dauke takardar sakin dana mata na yaga dana fahimci itace matar tawa, dan wallahi inason nazia baba fiye da yanda nakeson raina bazan iya ruyuwa ba itaba yana magana murya na sarqewa.!
Maigari yace alhamdulillahi dama munason muji gaskiyar magana, kuma gashi kun fada da bakinku. amma cikin maganganunku akwai abubuwan da ban ganeba.!
Kace lokacinda ka saketa bakasan itace matarkaba!!
Kenan kasanta tun farko kenan??
Itama tace baku taba saduwa da sunan aureba saidai.... sai ka hanata qarasa magana wanda yake nuna kamar kunsan juna kamin aure ko makamancin haka
Sai maganar ciki da kakeyi wanda kowa ya shaidi tanada ciki kuma akazo aka rasa cikin yanxu.
Ka nuna baka taba saninta ba baka ma taba ganinta ba ya akayi kasan tanada ciki?? Hakan ya nuna akwai wani boyayyen lamari da mu bamu saniba yanada kyau muma a mana bayani.!
Lokaci daya nazia da nura suka kalli juna kamar hadin baki sukace wallahi baba!!! sai dukansu sukayi shiru,, babu kom..... nan ma hada baki sukayi suka qara yin shiru nura ya qarasa maganar da cewa baba ba komai tsakaninmu baba!
Maigari dai bai gamsu ba sauran mutane ma tambayar maigari ta sakasu cikin tunani yanda suka hada baki ma ya nuna rashin gaskiyarsu a bayyane, yaya nura yace tunda dai munji haqiqan abin shikenan wani bincike bai tasoba baba koma miye wannan tsakaninsu ne rashin kyautawa ne dai nura ya riga yayi muna dada bada haquri. inaga shikenan kawai. anan dai akayita bada haquri akan qara abinda nura yayi aka shigo da maganar komawar nazia, yayan nazia yace abarta ta huta daga baya ayi wannan zancen, nazia da qarfin hali tace ni na bazan koma gidansa ba na amince idan na qare idda xan zamu daidaita da Dr mustafa idan mun shiryasai muyi aure.
Ke hulwaty..!!! Kinada hankali kuwa?? Kinsan abinda kike fada?? Da aurenki kina tunanin wani namiji ko?? Ta dalla mai harara da murguda baki aure kuma?? Ai yanzuu hulwa ta mai raboce haka suka fara musanyar magana sun ma manta akwai mutane tare dasu kowanne cike da kishi da bakin cikin rabuwa da dan uwansa!!
Harga Allah naxia dan ta bata masa rai tace zata aminta da Dr mustafa bawai dan tanasonsaba. Dukansu abin ya basu dariya yayan nura yace shikenan ya isa! Nura ya kalli yayansa cikin kwalla yace yaya kanajin abinda take cewa ko?? Nura yama manta da baya ma yayan nashi magana!! Tausayin qaninsa ya kamashi yace kayi haquri ta bari zamuyi magana daga baya.!
Haka dai abu ya qare, zaman baiwa nura dadiba idan ya tafi ina zai qara ganin hulwarsa. Kowa ya watse aka qara qaba....
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah yau wata shida abubuwa sun faru na baqin ciki da farin ciki nura ya zautu kamar bashiba ya dawo ustaz baya magana sosai abinci kadan yakeci ba wanda yake ganin walwalarshi yayi yayi akan hulwarsa ta haqura ammabina tqqi haqura. yayi kamun qafa gun yayanta sai yace ya nemeta su daidaita ta chanxa layi baya samunta. Jin dadinsa daya qin yuwar aurendu da Dr mustafa yanaga da mutuwa kawai zaiyi.
Naxooo tun kan ta qare idda yayanta ya samo mata admtn a dan fodiyo ta fara karatun ta amma soyayyar mijinta tana mata yawo akai ta tabbata har abada ba zaata daina son deen ba saidai tana barwa cikintane tunda ba yanda zatayi.....!
Kaji sona gaskiya.
ASHE KAINE MIJINA6⃣7⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Yau nazia ta fito lecture tare da sabuwar qawarta da tayi mai hankali da natsuwa Aysha ameen sokoto wacce haifaffiyar sokoto ce yarinyar nimw kaina jabo nq yaba da natsuwarta amma najma ake kiranta dashi yarinyar akwai ilimi kamar ana mata wahayi ga natsuwa da hankali, abinda yasa tasu taxo daya da nazia kenan duk da naxia akwai tsiwa amma tadan natsu yanxu.!
Suna tafe suna tadi har suka kawo gurin cin abinci sunyi letti ba sakwara gashi ita sukeson ci sai sukace to su fita wajen makarantar su siyo a motar najma ameen aka tafi motar sukaje Dady smart anan suka yada zango sunyi sa'a akwai sakwara a gun suna ci suna tadi anan nazia take cewa taji qamshin wani turare mai tayar mata da hankali yanayinta yadan chanza amma ta fuske kada najma uwar wayo ta ganota.! sunci sun qoshi, suna dati sama sama daga sama taji muryar da ko cikin bacci ko mutuwa tayi ta dawo taji muryar zata ganeta rabonda ta ji muryar wata shida kenan.
Muryar deen dinta ne yake kiranta hulwaty!!zunbur Ta miqe cike da mamaki ta kalleshi ya chanxa gaba daya. ya tara suma a fuska sai kuma ya mata kyau! chan ta tuna da chin mutuncin da ya mata ta daure fuska Malam lafiya?? Kawani xo ka tsayawa mutane akai.? Najma kinsan shine? Gurinki yaxone? Najma ta kurba malt ta kada kai alamar aah. Ta watsamai kallo da dara daran idonta masu rudar dashi tace to malam sai anjimako. Yaja ya tsaya yana kallon ikon Allah hulwa ce take nuna cewa bata sanshiba! Da taga ya kafe kamar an dasa ice sai ta zargu tacewa najma suje.
Suna kan hanya najma tana driving tace waye wannan mutumin na dazu?? Nima bansanshiba ta bata amsa a tsanake, Najma ta murmusa dama akwai wayo najma ko hanjin mutum tana gani! Amma acting dinki ya bayar dake naxoo, alamu sun nuna kunsan juna ! kuma kunyi kewar juna! kuma kunason juna! kuma kun tsani juna! kuma..... Is ok phycologist!@ ke haka kike kullum da fassara ni ko mai kama dashi ban taba ganiba sai yau najma ta qara murmusawa naxoo ki gaymin mana duk maganar da najma take bata kalli nazia ba tuqinta take hankali kwance, amma hajiya nazia hadda xufa dan kuwa ta rude tasan najma smart girl ce amma batayi xaton xata gane haka da sauriba. Sai ta basar da maganar. kai yaufa zamu shiga hannun Dr shu'aib kinsan bamuyi assignment dinsaba ko? Najma ta ganota sai ta shareta itama ta murmusa tace Eh yanxu muje muyi kamin mushiga lectr. ahaka har suka isa makaranta...
Naxia kam duk ta rude ganin deen tsohon abu ya dawo mata sabo, ta samu dagyar aka tashi ranar batayi bacci ba dan tunani!...
Nura kuwa binsu yayi a hankali har yaga inda suka shiga.
Tun daga ranar dan fodiyyo ta zamo mishi gida har ya gano department dinsu hulwarsa.
Ranar nazia ta fito shago ta siyo musu malt najma na hall tana jiranta sai kawai tayi kichibic da nura. Tsoro ya cikata. Haba hulwa miye duniya karki manta deen dinkine masoyinki mijinki...
Ta katseshi da daga hannu, ✋
That was then..! but now lost substances value & no regard before me.You are completely out of my mind, you are neither trusted nor reliable. Please find your way live me alone.!!
Bata jira amsarshiba ta qara gaba abinta malt dinda batasha ba kenan zuciyanta tana quna amma taji dadin maganganun da ta danna mai ko banxa tasan ya yaji haushi.. Najma ta kasa gane kan nazia qarshe naxia tasa kuka dagyar najma ta rarrasheta.!!
ASHE KAINE MIJINA??6⃣8⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Najma ta murmusa I know that. ! Na fahimci akwai wani abu tsakaninki da wannan guy din tun ranar. na barkine kawai dan naga bakyason maganar.! Amma miye aibi tunda yayi regret ku daida kanku mana?? Kinasonsa yana sonki mistk ba wanda ya wuce yinsa inaga kawai ki haqura nazooo ku maida aurenku. Ashe kin taba aure bansaniba.!! shine idan ana zancen banana kike fuskewa kinuna mana irin u don't now everything. Kai nazoo kin burgeni u are so smart more than me wallahi nazoo tadan dara batace komaiba.!
Haka najma tayita rarrashinta tana bata haquri har tadan saki rai suka rabu akan zatayi tunanin akan shawar da najma ta bata, koda ta aminta saita walfa nura..
Wannan karon ma nura ya tare nazia tare take da najma ya mata magana kamar yanda ya saba itama ta bashi amsa kamar kullum, ta nunashi da yatsa waike wane irin mutum ne?? And I won you not get to any of my bussinees any more.It also look like you don't have human conscious & moral values. Leaves for your own interest. Ta murguda baki ta wuce abinta.
Ran najma ya bace ba kadan ba, kuma tasan duk randa nazooo taga nura tamai cin mutunci sai tayi kuka tana dana sani abinda ta aikata Najma ta kalli nura ya bala'en bata tausayi sai ta wuce su dukansu tabar nazai ita kadai tayi kukanta har ta qare ba mai rarrashi....
Ran nazia ya bace wato najma laifinta ma take gani abinda takema nurako duk zata raba jaha dasu. Gobe sai taqi xuwa makaranta wasa wasa nazia saida tayi sati daya batazo skull ba ba nuraba hatta najma hankalin su ya tashi nura yaga najma ya daure ya tambayeta tamai bayanin rashin xuwanta ya bata haquri akan kada tayi fushi da aminiyarta akanshi. yakamata ta kira taji lafiyarta tunda bata saba fashin xuwa makatantaba. ya karbi number najma akan xata sanar dashi lafiyar nazoo idan sunyi waya.
Naxai kuwa ta sharawa inna qarya da yake inna ba yar boko bace tace sun sami dan hutune. Inna tahau ta zauna.
Bayan tafiyar nura najma ta kira nazia amma taqi dauka takira yafi sau biyar amma shiru ba labari, bayan lecture ta wuce gidan su nazoo. A palo ta sameta nazia ta daure fuska najma ta kwashe da dariya taja hannunta tana kwacewa har dai suka shiga daki. Ta ijiye jaka taje ta gaida inna ta dawo ta bude fridge ta samu malt daya ta bude zatasha nazoo ta kwace daga bakinta ta harareta tace: dan uwanki nura bai siyo mikiba!!? Maganar ta baiwa najma dariya tace ya siyomin gata a jaka ba sanyine ta bude jaka ta fito da malt ta bude xatashi naxia taqara kwace wai baza'asha abin nura a gidansuba. Najma kam dariya Abin yake bata dagyar ta samu naxoo ta dan saki jiki sukayi nagana ta fahimtar juna. Ta bata shawara har cikin ranta taji dadin maganar suka shirya suka dawo kamar basune suke rigima ba nazia har tana tambayar najma da gaske shi ya siya mata malt tace wasa takeyi wallahi ita miye hadinta dashi a hanya ta siya suka tafa ta tafi.... najma ta kira nura tamai baya ni nazia lafitanta lau da sauran bayanai kuma tace zata taimaka masa. amma bata nuna mai cewa naxia ta haquraba tadaice yaci gaba da addu'a kuma yaci gaba da mata magana...
Kamar kullum sun fito lecture tace a bari ta samo musu dan cake da malt susha da yake nazia mayyar malt ce ta hadu da wani course mate dinta da yake mutuwar sonta mai suna ahmad. ahmad Allah ya jarabceshi da son nazoo amma daidai da rana daya bata taba bashi fuskaba sama sama duke gaisawa yauma sun dai gaisa sai suka jera tare har shagon suka dawo. A kan hanya ya bata labarin ban dariya ta kyalkyale da daria dago kanta da zatayi sai taga deen gabansu ya daure fuska kamar ance maigari ya mutu. Keeeeee waye wannan?? Ashe bakida hankali bansaniba?? Kina da aurena akanki kike tsayawa tare da samari??
Kin manta........ shot your mouth up.! Don't ever called me matarka.! Am not & I will never be the one! So yafi kyau kasan inda dare ya maka!! Ta watsamai harara. ahmad yace malam an rasa hanyar da za'a bullone sai aka fake da cewa matanace so sai a nemi wata hanya bawannan ba. Naxoo ba tasan lokacinda ta kamo hannun ahmad ba tace muje ko baby na.!! Tuni idon nura sun rufe ya wanke nazia da wani wawan mari. Ahmad ya daga hannu zai rama mata nura ya riqe mai hannu..... Boy! Don't make the mistake of bullying me...! And for your information, you made a great mistake the other time because she's married to me, any time I sight you talking with her, you'll rest behind the bars...
Ya sakeshi da qarfi.
ASHE KAINE MIJINA6⃣9⃣
Na hauwa m. Jabo
By Alieyou_Abokie
Ta kalleshi ido cike da hawaye murya na rawa ta rasa abin fada mai yaji haushi, duk fasaha ta bace mata. I definitely loved you before I know your dirty hidden color. Learn your lessons as appropriate.... I really hate you deen...!!
Ta bi ta gefensa ta wuce ya rasa abin fada waima shi da yake neman sulhu mixai kaishi marinta?? Ya dungule hannu ya daki iska ya wuce abinshi. Abin mamaki nazia sai bata fadawa najma abinda ya faruba tunda tasan batada gaskiya kuma ta mata alqawarin xata daina wulaqanta nura.!
Tana xuwa tace miya tsayar dake haka tace fada na tsaya kallo security sukazo garin gudu aka bigemin fuska. ayyah sannu.!!
Tun daga ranar nura bai qara xuwa makarantarsuba harkwana hudu.! Nazia tadamu tana kallon cewa abinda ta masa ne yasa yaqi dawowa gashi ba halin magana,
Naxoo xamuje gidan uncle dina na karbo saqon umma please tunda bamuda lecture sai 4.. naxoo ta aminta sukaje, a hanya najma sai danne dannen waya take a mata sms itama tayi har suka isa gidan ba kowa maigadi ya gaidasu ya basu key suka shiga najma tace ta zauna ta kawo mata lemu. Ta kawo mata lemu ta shiga wani daki ta dauko wasu ledoji ta fita tace mata idan kun shirya ki mini waya inxo mu koma skull..!! Nazia ta miqe tsaye banganeba malama mi..... ta budebaki da mamaki miya kawo nura nan gidan?? Yasa key ya kulle qofar ya maida key aljihu ya matso kusa da ita tsoro da mamaki suka kamata wato set up ne suka mata ko??
Ta rasa bakin Magana sai ta nemi guri ta zauna. Nura ya matso kusa da ita ya tsuguna yana fuskantarta qamshin turarensa ya daga mata hankali amma ta fuske.... nura ya fara bata haquri akan marin da ya mata a skull gaban saurayinta, nifaba saurayina bane! Ok. Koma miye kiyi haquri ta kawar dakai. Nura ya shiga aikin rarrashin nazai yana magana yana kuka alamu sun nuna yayi dan dana sanin abinda ya aikata. Ita dama tuni ta yafemai kodan ganin halin da ya shiga, (( kaji mace idan dai tanason namiji tsakani da Allah wallahi komai ya mata zata haqure)) batace dashi komaiba ganin ya tsananta kukanshi ne sai taga rashin dacewar haka yana namiji yaxo yana mata kuka tace shikenan ya wuce!! Ya dago jajayen idinsa ya kalleta nazai kice kin yafemin mana!! karo nafarko da ya taba kiranta da nazai saidai hulwaty....!!
ASHE KAINE MIJINA 7⃣0⃣
Na Hauwa M. Jabo.
By Alieyou_Abokie
Batasan lokacinda ta fashe da kukaba ta dora kanta akan cinyoyinta tana rera kuka.! Hankalin nura yayi matuqar tashi ganin kukan hulwarsa baisan sanda ya rungumota jikinsa ba yana rarrashi tana shaqar qamshin turarensa hankalinta yana neman gushewa a jikinta batayi qoqarin kwace kantaba taci gaba da kukanta da sauti. tana kwance a jikinta shiko yana ta rarrashinta yana bata magana yana jadda damata ya karbi kuskurenshi bazai iya rayuwa idan bataba, tana kuka tayi qasa da murya daidai kunnensa tamai magana kamar rada, deen u betrayed my life! U really hurt and harm my life because my heart insisted & become mad in your love.!! It's not an exergration that i can't do with out you. I remain yours no shacking I sincerely love you.!
Deen please kada ka qara barina please!!
Ya qara matseta a jikinsa, ya rada mata a kunne
Hulwaty..!! I can't leave you! You're my life, sight. I wholeheartedly love you. Your love is in my blood. me all my short comings, I will never repeat it again.!
Ta qara lafewa a jikinsa batace komaiba taci gaba da kukanta yana shafata yana rarrashi nidai jabo na saki baki ina kallonsu abin yana bani mamaki wai har sun shirya! dama ance tsakanin mata da miji sai Allah, da nice da ba haka kam😕...
Sun fahimci junansu sun yafi junansu a hankili ta janye jikinta daga cikin nashi yace kin gaji dani ne tamai murmushin nan da yayi watanni bai ganiba ya shafa fuskarta daidai dimple dinta shima yayi murmushi. Suka share hawayen Junansu suka dan taba hira chan nazia tace: najma fa tana jiranmu, deen yace nifa har na manta da ita! Lallai deen duk taimakon da ta maka shine zaka manta da ita? Waima ya akayi kukayi wannan tunanin?? Ba ruwanki sirrine tsakaninmu.! Su rirri manya koda muka fito sai mukaga bashir da najma suna soyewa..( aruwar jabo najma da basheer suna burgeni da sunyi aure da saina rubutomuku labarinsu.)
Sannunku fa, laaaa kinga ni har na manta da ku. U see.. da deen ma yace ya manta dake! Laa hulwa banda sharri fa yaushe nace na manta da najma, ai ni banida kamar najma a fadin duniyar nan. Duk muka kwashe da dariya....
Mun koma makaranta cike da farin ciki na baiwa najma labarin abinda ya faru tanajin dadi har tana cewa yaushe zamusha biki!
************
ASHE KAINE MIJINA 7⃣1⃣
NA HAUWA M JABO.
By Alieyou_Abokie
Wata sabuwar soyayyah akeyi tsakanin nura da nazia kamar ba abinda ya taba shiga tsakaninsu nima dai hauwa jabo suna burgeni kuma ina daukar darussa a love dinsu kamar su hadiye juna. Haka zaka gansu kamar wasu budurwa da saurayi, amma duk da haka naxia akwai abinda bata yi dan kawai tsare gida.!
Nura yama mai gari magana akan sun daidaita da nazia zasu maida aurensu kowa yayi farin ciki da haka bada bata lokaciba aka maida aurensu nan ma anyi sabuwar bidi'a auren soyayyah...!!
Daren ranar nura ya tuhumi nazia akan xubar mai da ciki da tayi kamin ta gane shine mijinta aranta tace ASHE KAINE MIJINA bansaniba! sabida haka yau sai ya tabbatar da cewa ya sami wani yaron. bata bashi amsaba dan tasan bata zubar da cikin ba tayi niyya sai Allah yayi nasa ikonn. sai bayan sati daya tace ya rakata asibiti yana mamakin mi ya sameta tace sudaije a sibiti takaishi gun Dr da ya dubata anan Dr yama nura bayanin cewa ba zubar da cikin akayiba zubewa yayi da kanshi sanadiyar damuwa da tashiga da kuma rashin lafiyar yaron kuma ya gaya musu dagyar ma idan xata qara samun ciki hankalin nura ya tashi dajin haka Dr ya kwantar mai da hankali da cewa akwai magungunan da takesha tana qarewa zata warke zata samu ciki. Haka kuwa akayi nazia tun daren farko data koma samu wani cikin. Soyayyah suke kamar su hade juna suna girmama juna.!!
Sun shiryaa da sister khadee amaryar ammar, kamar basu ba haka qawancen su da najma sai abinda ya qaru dan nazia nason najma. dan itace sanadin maido mata da farin cikin ta, so tana mata fatan samun yaya bashir dinta. zainb khalifa kuwa uwar kuri da iyayi kullum tana min waya ya baby irin dai ana neman gindin zama gun nazia wai ita dangin miji....
Naxia da nuraddden kullum cikin farin ciki suke Cikin ikon Nazia ta haifi yayanta uku duk maza AHMAD HAMEED MAHMOUD. yayan abin son kowa kyawaonsu ma ya wuce misali nima jabo nayi kamen daya da yata dazan haifa idan nayi aure.. ummulkhairi qarin jini ma tayi kamun daya da yarta mai shan nono.....
The End!!!
0 Comments